Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya da ya je yakin duniya ya koka da kin biyansa Fansho

Sojin Najeriya da ya halarci yakin duniya na II
Sojin Najeriya da ya halarci yakin duniya na II Solacebase

Wani tsohon sojin Najeriya da ya halarci yakin duniya na biyu Adamo Aduku ya bukaci gwamnatin kasar ta taimaka ta biya shi hakkokinsa na Fansho.

Talla

Adamo Aduku wanda yanzu haka ke da shekaru 104 a duniya, na daga cikin tsaffin jami’an Sojin da babban Hafson Sojin Najeriyar ya karrama yayin wani biki a ranar tunawa da ‘yan mazan jiya da ya gudana a Lagos.

Da ya ke Magana da manema labarai, Adamo Aduku ya ce tun bayan da aka sallameshi daga bakin aiki cikin shekarar 1957 har yanzu bai samu hakkokinsa na barin aiki ba.

Cikin jawaban Aduku gaban Manema, ya ce tun cikin shekarar 1942 ya shiga atawagar dakarun yammacin Afrika da aka yi amfani da su a yakin duniya na 2, inda kai tsaye aka zuba su a jiragen ruwa zuwa India suka gwabza yaki a Calcutta.

A cewar Tsohon sojin na Najeriya bayan dawowarsu gida a shekarar 1946 sun shiga tawagar horarwa a Lagos kafin daga bisani a sallame su a cikin shekarar.

Adamou Aduku y ace, a cikin shekarar 1950 ya sake koma aikin soja kafin a sake sallamarsa a 1957, matakin da ya tilasta masa komawa fagen noma can a kasarsa ta haihuwa wato karamar hukumar Ibejukolo Omala ta jihar Kogi.

Tsohon sojin na Najeriya Adamo Aduku ya bayyana cewa kawo yanzu bai taba samun ko sisi a matsayin Fanshinsa ba, a don haka ya ke neman gwamnati ta agaza masa wajen biyansa hakkokinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.