Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya yi karin girma ga wasu hafsoshin Soji saboda samar da tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari o.obasa.jpg

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yiwa wasu manyan hafsoshin sojin kasar karin girma na musamman saboda gagarumar rawar da suka taka wajen aikin samar da tsaro.

Talla

Sanarwar da Daraktan yada labarai na ma'aikatar tsaron Najeriya, Kanar Sagir Musa ya sanyawa hannu ta ce an karawa Manjo Janar Lamidi Adeosun girma daga mukamin sa na yanzu, zuwa Laftanar Janar, yayin da aka karawa kwamnadan runduna ta 7 Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu girma zuwa Manjo Janar.

Sanarwar ta kuma ce an karawa Laftanar AJ Danjibrin girma zuwa Kaftin.

Sanarwar ta kuma ruwaito babban hafson sojin Najeriyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai na ta ya murna ga hafsohin dangane da karin karin girmar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.