Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe kawun dan Majalisar Dattawan Najeriya

Dan majalisar dattawan Najeriiya Ishaku Abbo
Dan majalisar dattawan Najeriiya Ishaku Abbo RFI-h

‘Yan bindiga sun kashe kawun Dan Majalisar Dattawan Najeriya Ishaku Abbo tare da yin garkuwa da babarsa mai suna Rafikatu Ishaku ranar asabar da ta gabata a jihar Adamawa

Talla

Majiyoyi sun ruwaito daga shaidu cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a gidan dan Majalisa Abbo da ke Muchalla a karamar hukumar mulkin Mubi ranar asabar 13 ga watan Yuli, inda suka yi awun gaba da babarsa, sannan kuma suka kashe kawunsa lokacin da ya fara ihu domin neman ceto.

Jami’in hulda da jama’a a rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Sulaiman Nguroje, ya ce lamarin ya faru ne da asubah, sannan ya ce yanzu haka suna ci gaba da kokarin ganin wadanda suka tafka wannan ta’asa.

Lamarin ya faru ne kasa da mako daya bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Sakataren Dindindin na ma’aikatar kwadagon jihar, inda suka bukaci a biya Naira milyan 25 kafin sakin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.