Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Yakubu Haruna Ja'e kan sabuwar wasikar Obasanjo ga shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Sauti 03:50
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo AFP PHOTO / SEYLLOU

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya sake aike wa da shugaban kasar, Muhammadu Buhari wata wasika, inda a cikinta yake kashedin cewa kasar na daf da dulmiyawa cikin rikici, wanda shi shugaban Najeriyan ne kadai zai iya ceto ta.Obasanjo wanda ya mulki kasar a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya ce an samu rarrabuwar kawuna irin wanda ba a taba samu ba a kasar a lokacin gwamnati mai mulkin kasar a yanzu. Michael Kuduson ya zanta da Dr Yakubu Haruna Ja’e, masani kuma mai sharhi kan siyasa da alakar kasashe a jami’ar jihar Kaduna a Najeriya kan wannan wasika.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.