Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Zuma na fuskantar barazana

Jacob Zuma Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu
Jacob Zuma Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko

Tsohon Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma yace ya samu wasiku dake barazana ga rayuwar sa bayan ya fara bayyana a gaban hukumar gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da aka fara a wannan makon.

Talla

A zama na biyu da hukumar tayi jiya talata, tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya shaidawa shugaban hukumar cewar shi da iyalan sa sun samu sakwannin dake barazana ga rayuwar su.

A cigaba da tambayoyin da ake yiwa tsohon shugaban, Zuma yaki amincewa da zarge zarge da dama da kuma kusancin sa da iyalan gidan Gupta, attajiran da ake zargi da hannu dumu dumu wajen ayyukan cin hanci a Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.