Isa ga babban shafi
Afrika

Kusan mutane miliyan 3 a zagayen tafkin Chadi na bukatar tallafi - MDD

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres TONY KARUMBA / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane kusan miliyan 3 dake zama kusa da tafkin Chadi ne ke bukatar kariyar tsaro da kuma tallafi sakamakon illar rikicin Boko Haram.Daraktan Hukumar Cigaba na Majalisar dake kula da Afirka, Ahunna Eziakonwa ta bayyana haka wajen taron Gwamnonin dake kewaye da Tafkin Chadi da kuma masana harkar tsaro da wakilan kungiyoyin fararen hula a Nijar.

Talla

Taron da hukumar dake kula da tafkin Chadi ta shirya tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya zai mayar da hankali ne kan matsalar da rikicin Boko Haram ya haifar a Yankin da kuma lalubo hanyar rage radadin matsalar ga mazauna yankin.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniyar, Ahunna Eziakonwa ta ce rikicin na Boko Haram bayan sanadiyar rasa dimbin rayuka da kuma asarar dukiyoyi, ya kuma lalata dangantakar da tsakanin al’ummomi da kuma jefa rayuwar talakawa cikin mawuyacin hali.

Jami’ar ta ce mutane miliyan 19 ke rayuwa kusa da tafkin Chadi daga Jihohi 8 na kasashe 4 dake da al’adu da yare da kudin bai daya da suke musaya a tsakanin su.

Eziakonwa ta ce da taimakon kasashen Jamus da Sweden, Majalisar Dinkin Duniya na daukar matakan tallafawa mazauna wannan yankin daga kasashe 4 dake kewayen tafkin Chadin domin inganta rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.