Isa ga babban shafi
Sudan

An kammala kulla yarjejeniyar mika mulki ga farar hula a Sudan

Dandazon masu zanga-zanga kenan da ke murnar kammala kulla yarjejeniyar mika mulki ga farar hula a Sudan
Dandazon masu zanga-zanga kenan da ke murnar kammala kulla yarjejeniyar mika mulki ga farar hula a Sudan REUTERS/Umit Bektas

Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta tabbatar da kammala kulla yarjejeniyar fahimtar juna tare da mika mulki ga farar hula tsakanin bangaren Soji da jagororin masu zanga-zanga a Sudan.

Talla

Bayan sanar da matakin a yammacin juma'a, dubban al’ummar kasar ta Sudan ne suka fita tituna don nuna farin cikinsu da yarjejeniyar wadda ilahirin bangarori biyun suka amince da ita.

An dai kulla yarjejeniyar ne karkashin makamanciyarta da bangarorin biyu suka sanyawa hannu ranar 17 ga watan Yuli wadda ta aminceda kafa gwamnatin hadaka tsakanin Sojin da farar hula zuwa nan da shekaru 3 masu zuwa.

Da ya ke jawabi gaban manema labarai, Mohammed El Hacen wakilin kungiyar AU da ke shiga tsakani a rikicin kasar ta Sudan, ya ce an yi nasarar cimma yarjejeniyar wadda bangarorin biyu suka amince bayan shigowar kungiyar ta AU da wasu kasashen duniya.

A cewar wakilin na AU, yanzu haka taruka fahimtar juna ne suka ragewa bangarorin biyu don sanin ta yadda za su tsara aikace-aikace da kuma raba mukamai da ake fatan a kammala cikin lumana.

Suma dai bangaren masu zanga-zangar yayin sanya hannu gaban wakilan kasa da kasa a yau Asabar sun bayyana cewa, a gobe Lahadi ake fatan yarjejeniyar ta fara aiki gadan-gadan.

Tattaunawa tsakanin jagororin masu zanga-zangar da banagren Sojin da ke mulkin kasar dai ya yi ta cin karo da matsaloli a baya-bayan nan biyo bayan zarge-zargen take hakkin farar hula ciki har da kisan masu zanga-zangar.

Ko a makon jiya jagororin sun janye daga tattaunawar bayan fitar wani rahoto da ke nuna yadda jami’an tsaron kasar suka kashe farar hula 127 yayin zanga-zangar ranar 3 ga watan Yuni.

Sudan dai ta tsinci kan ta cikin rikici ne kusan watanni bakwai da suka gabata, wanda ke da alaka da tsadar rayuwa baya ga hauhawar farashi, matakin da ya kai ga hambarar da gwamnatin shugaba Omar Hassan al-Bashir da ya shafe kusan shekaru 30 ya na mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.