Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan: Sojoji da farar hula sun kafa gwamnatin hadaka

Wakilan masu zanga-zanga da na sojojin Sudan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Wakilan masu zanga-zanga da na sojojin Sudan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa. AFP/Ebrahim HAMID

Dubban jama’a a Sudan na gudanar da bukukuwan murna musamman a Khartoum babban birnin kasar, bayan nasarar rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka tsakanin sojojin dake mulkin kasar da farar hula a yau asabar.

Talla

Sai dai ruguntsimin murnar na gudana ne tare da tunawa da wadanda suka rasa rayukansu, yayin zanga-zangar da dubban yan kasar suka shafe watanni suna yi, domin tilastawa sojoji da suka kawar da gwamnatin Omar al-Bashir, mikawa farar hula mulki.

Gwamnatin hadin gwiwar da aka cimma yarjejeniyar kafawa za ta shafe shekaru uku tana mulki, kafin shirya zaben mika mulki, ga cikakkiyar gwamnatin farar hula.

Tarin jama’a daga kasashen masu mawabtaka da kasar ta Sudan sun dunguma zuwa Khartoum don taya ‘yan kasar murnar zaman lafiyar da aka samu.

Mataimakin shugaban majalisar mulkin sojojin na Sudan Muhd Hamdan Daglo da kuma Ahmed al-Rabie, dake wakiltar masu zanga-zanga ne suka jagoranci sa hannu kan yarjejeniyar yau asabar a birnin Khartoum, taron ya samu halartar manyan wakilan gwamnatocin kasashe da dama.

Wannan nasara dai ta kawo karshen rikicin siyasar kasar ta Sudan da ya lakume rayukan akalla mutane 250.

Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar ce karkashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Afrika da kasar Habasha bayan shafe watanni da dama da kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata.

Gamayyar jam’iyyun adawa a Sudan sun cimma matsayar zabar Abdalla Hamdok, tsohon babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, domin nada shi a matsayin Fira Ministan gwamnatin hadin gwiwa tsakanin sojoji da farar hula, da zata shafe shekaru 3.

Jam’iyyun adawar na Sudan, sun kuma zabi Muhd AlHafiz Mahmud da AbdelQadir Muhd Ahmd, a matsayin babban jami’i mai shigar da kara, da kuma shugaban sashin shari’ar kasar, wadanda ake sa ran nada su a ranar litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.