Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan adawa sun zargi gwamnatin Mnangagwa da mulkin kama-karya

Wani mai zanga-zanga kwance a kasa, bayan dukan da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi masa.
Wani mai zanga-zanga kwance a kasa, bayan dukan da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi masa. AFP/Zinyange Auntony

‘Yan sandan sun yi amfani da kulake da kuma hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa dandazon ‘zanga-zanga jiya Juma’a a Zimbabwe, wadanda suka bijirewa umarnin kotun kasar na haramta gudanar da gangamin.

Talla

Masu zanga-zangar da suka taru a babban birnin kasar Harare, duka da girke dubban jami’an tsaro, sun zargin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa da gazawa wajen magance matsalar kangin talaucin da kasar ke dada nutso a ciki.

Da fari ‘yan sanda tun tarwatsa gangamin dake karkashin jagorancin babbar jam’iyyar adawa ta MDC, ta hanyar duka da kulake, kafin amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi, matakin da yasa, ‘yan adawa suka zargi gwamnatin shugaba Mnangagwa da zarta ta Robert Mugabe mai murabus, kama-karya.

A farkon watan Agusta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shirin neman tallafin dala miliyan 331 don kai daukin gaggawa ga al’ummar kasar Zimbabwe fiye da miliyan 5 da ke fuskantar tsananin yunwa.

Shirin wanda hukumar kula da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar a jiya, ta ce zai agazawa kashi 1 bisa ukun al’ummar Zimbabwe da ke fuskantar matsananciyar yunwar tsawon lokaci sanadiyyar farin da kasar ke fama da shi dama mashassharar da tattalin arzikinta ke fuskanta.

A cewar Majalisar, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, za a iya fuskantar karin mutane miliyan 5 da yunwar za ta shafa a kasar ta Zimbabwe cikin shekara mai zuwa, sakamakon yadda farashin abinci ke kara yin tashin gwauron zabi baya ga karancin abincin sanadiyyar fari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.