Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan za ta kaddamar da majalisar zartaswar gwamnatin hadaka

Wakilan farar da sojoji masu mulkin Sudan yayin sa hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Wakilan farar da sojoji masu mulkin Sudan yayin sa hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa. AFP/Ebrahim HAMID

Sudan za ta kaddamar da majalisar zartaswar sabuwar gwamnatin hadaka, mataki na farko bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da farar hula.

Talla

Sabuwar majalisar zartaswar ta Sudan za ta kunshi farar hula 6 da kuma sojoji biyar.

Bangaren sojoji ne kuma zai soma jagorantar mulkin gwamnatin hadakar na tsawon watanni 21-yayinda bangaren farar hula zai karasa jagorancin watanni 18, kafin mika mulki ga cikakkiyar gwamnatin farar hula a shekarar 2022.

Tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar asabar ake runguntsimin bukukuwa a sassan kasar, musamman a birnin Khartoum.

A ranar talata ake sa ran rantsar da Abdalla Hamdok, tsohon babban jami’in majalisar dinkin duniya, a matsayin Fira Ministan Sudan, bayan da gamayyar jam’iyyun adawa a kasar suka zabe shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.