Isa ga babban shafi

'Yan sandan Najeriya sun sake kame jagoran 'yan garkuwa da mutane

Fitaccen dan garkuwa da mutane a Najeriya Hamisu Wadume
Fitaccen dan garkuwa da mutane a Najeriya Hamisu Wadume NAN

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da sake kame Hamisu Wadume mutumin da hukumomin tsaron kasar ke zargi da jagorantar ayyukan garkuwa da mutane, bayan kubcewarsa makwanni 2 da suka gabata, bayan da sojoji suka bude wuta kan jami'an 'yansandan da suka kamo shi.

Talla

Tun a ranar 6 ga watan nan ne ‘yan sandan Najeriyar suka yi nasarar kame Wadume a Jihar Taraba amma kuma ya kubce a lokacin da suke kokarin kai shi babban Ofishinsu da ke Jalingo bayan da wasu Sojoji suka budewa motarsu wuta tare da hallaka manyan jami’an ‘yansandan sashe na musamman da ke yaki da manyan laifuka 3 da kuma wani farar hula1.

Rahotanni sun bayyana cewa a daren jiya Litinin ne ‘yan sandan suka sake nasarar kame Wadume a jihar Kano da ke arewacin Najeriyar tare da mika shi ga Shalkwatar ‘yan sandan ta kasa.

Cikin bayanan da Wadume ya gabatar gaban Manema labarai a Najeriyar, ya tabbatar da sa’insar da ta faru tsakanin wasu sojoji da ke tsaron hanya da kuma ‘yan sandan wanda ta kai ga bude wuta ga tawagar ‘yansandan ta musamman da ta jagoranci aikin kame dan garkuwar.

Mr Wadume ya bayyana cewa Sojojin bataliya ta 93 ta rundunar Sojin Najeriyar da saninsu suka bude wuta kan tawagar jami’an ‘yansanda tare da hallaka mutum 4 ciki har da farar hula daya kafin daga bisani su bashi damar guduwa.

A jawaban da ya gabatar ta cikin wani faifan bidiyo da shalkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta fitar a yau Talata ya ce Jami’an Sojin da kan su suka yanke ankwar da ke hannunsa tare da umartarsa da ya gudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.