Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Aliyu Idi Hong kan yadda hare-haren kin jinin baki ya tsananta kan 'yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu

Sauti 03:40
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu Pulse

Gwamnatin Najeriya ta ce hakurinta ya kare kan irin hare haren da Yan Afirka ta kudu ke kai wa kan 'yan kasar ta da ke zama acan, inda su ke kona masu shaguna da kuma sace kayayyaki.Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana haka a sakon da ya aike ta kafar twitter inda yake cewa kasar ba zata lamuncewa yadda wasu bata gari ke kai hari kan yan kasar ba. Wannan mataki ya biyo bayan harin da aka kaiwa Yan Najeriya a karshen mako inda aka kasha 3 daga cikin su, kana aka kona shagunan su a unguwar Jeppestown dake Johannesburg.Hakan ya sa muka tattauna da Dr Aliyu Idi Hong tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ga kuma tsokacin da ya yi mana.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.