Isa ga babban shafi

Guterres ya bukaci karfafa rundunar G5 Sahel

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres REUTERS/Brendan McDermid

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci tallafawa asusun yaki da ta’addanci a kasashen yankin Sahel yana mai cewa babu yadda za a yi yakin ya yi nasara har sai an hada hannu ta kowacce fuska.

Talla

A wata zantawarsa da sashen labarai na RFI yayin ziyarar da yanzu haka ya ke a kasar Congo, Antonio Gutteress ya bukaci hada hannu don tallafawa rundunar G5 Sahel da ke yaki da ta’addanci a kasashen yankin 5.

A cewar Guteress kawo yanzu babu alamun nasara a yakin da ta’addanci cikin kasashen 5 wanda ya zama wajibi a mike tsaye don kara karfafa rundunar ta kowacce fuska.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterss ya kuma gwada misali da hare-haren baya-bayan nan kan dakarun Soji a kasar Burkina Faso, wadda ke matsayin guda cikin kasashen yankin 5 da suka kunshi, Chad, Mali da kuma Nijar baya ga Mauritania wadanda ke fama da hare-haren ta’addanci daga mayaka masu ikirarin jihadi da kuma ‘yan bindiga dadi.

Karkashin jagorancin Faransa ne dai aka samar da runduna ta musamman mai dauke da dakaru dubu 5 don yaki da ta’addanci a kasashen na Sahel 5, sai dai Antonio Gutteress ya ce yanzu batun na bukatar tallafin sauran kasashen duniya don samun cikakkiyar nasara a yaki da ayyukan ta’addancin.

A cewar Gutteres akwai bukatar samun cikakken tallafin da rundunar ke bukata yayin babban taron kasashen yammacin Afrika da zai gudana a birnin Wagadugu, ta fuskar tallafin kudaden dama dakarun da za su dafa a yakin da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.