Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Tsohon shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya rasu

Tsohon Shugaban Zimbabwe marigayi Robert Mugabe
Tsohon Shugaban Zimbabwe marigayi Robert Mugabe Phill Magakoe / AFP

Tsohon shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya rasu ya na da shekaru 95 a  Singapore kamar yadda shugaban kasar mai ci, Emmerson Mnangagwa ya sanar a sanyin safiyar yau Juma'a

Talla

Mugabe ya shugabanci kasar daga shekarar 1980 zuwa 2017, yayinda ake danganta shi da mulkin kama-karya.

Mugabe ya fuskanci boren 'yan siyasa da kungiyoyi a kasarsa a wani lokaci da jama’a suka gano cewa ba shi da karfin tafiyar da mulkin kasar saboda tsufa,yayinda wasu ke hasashen cewa matarsa Grace Mugabe na yin katsalandan kan harakokin gwamnatin kasar da na siyasa.

Sojoji da wasu tsoffin zarata da suka yi gwagarmayar neman 'yancin kasar tare sun  tilasta masa sauka daga kujerar shugabancin kasar a shekara ta 2017.

An haifi Robert Mugabe ranar 21 ga watan Fabarairu shekarar 1924 a Kutama a tsofuwar Rhodesie ta kudu da ta canza suna zuwa Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.