Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Za a kaddamar da ayyukan ci gaba a garin Tillaberi a Jamhuriyar Nijar

Sauti 03:45

A Jamhuriyar Nijar, kamar dai kowace shekara, 18 ga watan disamba ita ce ranar da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar jamhuriya.A kowace shekara, shugaban kasar ta Nijar na amfani da wannan rana domin kaddamar da muhimman ayyukan irin na ci gaba a daya daga cikin jihohin kasar, da suka hada da hanyoyi, gidaje, filayen wasa da dai sauransu.A bana za a gudanar da binkin ne a garin Tillaberi da ke yammacin kasar, wanda aka yi wa take da ‘’ Tillaberi Tchandalo’’.Amadou Moussa da ake kira da suna Amede, mai bayar da shawara ne na musamman ga shugaban kwamitin shirya wannan biki, ya yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.