Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane 57 sun mutu sanadiyyar Ambaliyar ruwa a Nijar

Wani yanki da ya fuskanci ambaliyar ruwa a Nijar
Wani yanki da ya fuskanci ambaliyar ruwa a Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

Wasu sabbin alkalumman da mahukuntan kasar Nijar suka fitar a jiya Talata, sun tabbatar da mutuwar mutane 57 a sanadiyyar ambaliyar ruwa yayin da wasu karin dubu dari da talatin suka rasa matsugunansu daga farkon watan Yuni zuwa yau.

Talla

Acewar wata sanarwa da aka fitar yayin taron ministocin kasar a jiya talata, ta bayyana cewa sakamakon karshe da gwamnati ta tattara ya nuna mutun 57 ne suka mutu yayin da wasu mutane dubu 132 da dari 5 da 28 suka tagayyara kwatam-kwacin iyallai dubu 16 da 93.

Ko baya ga haka ambaliya ruwan ,ta lalata gidaje dubu 12 da dari 241, haka zalika ta kuma lakume rayukan dabbobi dari 851 tare da salwantar Hekta dubu 2 da 251 na filayen noma.

Acewar alkalumman, ambaliya ruwan tafi barna a jihohi Maradi da Zinder, sai kuma jihohi yamai, Dosso da ke biya musu baya.

A wani abun da ba sabo ba, yankin arewacin kasar mai yanayi irin na hamadar sahara shi ma ya samu nasa rabon na ambaliya ruwa a wannan karon inda ta daidaita sama da mutun dubu 18.

Wadanan sabbin alkalumman dai sun sha banban da wadanda ministan kula da ayukkan bada agaji na kasar ya fitar a farkon watan Satumba nan inda ya ce mutum 47 ne suka mutu yayinda wasu dubu 70 kuma suka rasa matsugunansu.

Har yanzu dai ana ci gaba da samun saukar ruwan sama a wasu sassan kasar ta Nijar duk da karancin lokutan da daminar ke da shi abun da ke kara haifar da damuwa a zukatan wasu al’umomi kan yiyuwar sake fuskantar ambaliya ruwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.