Isa ga babban shafi
Afrika

Masu zanga-zanga sun kashe shugaban 'yan sanda a Mali

Yan Sanda a kokarin su na tabatar da tsaro a Tombouctou
Yan Sanda a kokarin su na tabatar da tsaro a Tombouctou AFP/PHILIPPE DESMAZES

Wasu masu zanga-zanga a garin Niono dake da nisan kilometa 270 da Bamako babban birnin kasar Mali sun halaka shugaban yan Sanda na garin da ake zargi da kuntatawa jama’a.

Talla

Kisan jami’in da kungiyar kare hakkokin yan Sanda ta kasar ta yi Allah wadai na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da fuskantar rashin tsaro a garin Tombuktu inda mutane da dama suka samu rauni biyo bayan fada tsakanin kabilu mazauna garin ranar Laraba da ta gabata.

Rahotanni daga masu bincike na nuni cewa mutanen garin sun afkawa barikin yan Sanda na garin Niono, inda suka bukaci an canza musu shugaban yan Sandan, kafin daga bisali sun dinga jifar ginin da duwatsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.