Isa ga babban shafi
Masar

Zanga-zangar adawa da al-Sisi ta sake barkewa a Masar

Masu zanga-zangar adawa da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi.
Masu zanga-zangar adawa da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi. AFP

Zanga-zangar neman tilastawa shugaban Masar Abdelfattah al-Sisi ta sake barkewa karo na biyu a Masar, duk da kamen da jami’an tsaro suka yiwa wadanda suka soma zanga-zangar a ranar Juma’a.

Talla

A jiya asabar zanga-zangar adawa da al-Sisin ta juye zuwa tarzoma, bayan da fada ya barke tsakanin jami’an tsaro, da kuma wani gungu na jama’ar da suka fita a birnin Suez, inda ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye gami harbi kan masu zanga-zangar.

Har yanzu dai daruruwan jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a filin taro na Tahrir, cibiyar gagarumar zanga-zangar farko da ta kawo karshen mulkin tsohon shugaban Hosni Mubarak.

Zanga-zangar da Misirawan ke yi na da nasaba da matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin al-Sisi ta dauka tun a shekarar 2016, bayan amsar bashin dala biliyan 12 daga asusun bada lamuni na duniya IMF.

Wani rahoton masana tattalin arziki da aka wallafa a cikin watan Yulin da ya gabata, ya ce kusan mutum guda cikin uku a Masar, yana rayuwa kan kasa da dala 1 da rabi a rana, yanayin dake nuni da matsin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.