Isa ga babban shafi
Faransa- Sudan

Faransa za ta bai wa Sudan kudin sake gina kasar

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaban Faransa Emmanuel ya ce, kasar za ta taimaka wa Sudan da kudaden da yawansu ya kai Euro milyan 60 a matsayin gudunmuwarta domin sake gina kasar.

Talla

Shugaba Macron wanda ke ganawa da Firaministan kasar ta Sudan Abdallah Hamdok, ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin cewa Sudan ta koma cikakken tsarin dimokradiyya tare da ganin cewa Amurka ta cire kasar daga cikin jerin wadanda ke mara wa ayyukan ta’addanci baya.

A ranar Litinin Firaminista Hamdok, ya gana da kwamandan daya daga cikin kungiyoyin ‘yan tawayen yankin Darfur Abdel Wahid Nur a birnin Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya tsara wannan ganawa tsakanin sabon Firaministan da kuma madugun ‘yan tawayen don samar da zaman lafiya a Sudan wadda ta bude sabon babin mulkin dimokraiyya bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.