Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya na neman dakarunta 22 da suka tsere daga bakin daga

Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan sojin Najeriya.
Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan sojin Najeriya. Nigerian Army

Rundunar Sojin Najeriya tayi shelar neman dakarun ta 22 da ake zargin sun gudu daga inda ake yaki da kungiyar boko haram, kuma ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda suka shiga.

Talla

Rahotanni sun ce bisa ka’idar aikin soji, wadannan sojoji 22 na iya fuskantar hukunci mai tsanani na tserewa daga wurin yaki idan an same su, ba tare da gabatar da hujja mai karfi ba kan dalilin batar su.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta jiyo daga wasu kwamandodin sojin dake yaki a bakin daga da suka bukaci sakaye sunan su cewar, sojojin da ake nema sun gudu ne daga Gubio ranar 29 ga watan Satumba, bayan wani hari da aka kai wanda yayi sanadiyar kashe sojoji 18.

Jaridar tace rundunar sojin Najeriya taki cewa komai kan sojojin da suka jikkata ko kuma aka kasha lokacin harin, amma bayan tantance dakarun dake wurin bayan harin, an gano cewar 22 sun bata, ba tare da sanin inda suka shiga ba.

Cikin jerin sunayen da Jaridar ta wallafa na sojin da suka gudu sun hada da mai rike da mukamin Manjo guda da saje saje da kofur da mataimakin kofur da kuma kurtu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.