Isa ga babban shafi
Nijar - Amurka

Amurka ta kaddamar da farautar al-Sahrawi

Dakarun Amurka dauke da gawar daya daga cikinsu da suka halaka a kauyen Tongo Tongo dake Jamhuriyar Nijar.
Dakarun Amurka dauke da gawar daya daga cikinsu da suka halaka a kauyen Tongo Tongo dake Jamhuriyar Nijar. Reuters

Amurka ta dauki alkawarin biyan ladan dala miliyan 5, ga duk wanda ya taimaka mata da bayanai kan shugaban reshen kungiyar IS a yankin saharar Afrika, da yayi ikirarin kashe dakarun Amurkan da na Jamhuriyar Nijar shekaru 2 da suka gabata.

Talla

Amurka ta kaddamar da farautar Adnan Abu Walid al-Sahrawi ne bayanda ya dauki alhakin farmakin da mayakan IS suka kaiwa dakarun hadakar Amurka da Nijar a kauyen Tongo Tongo, ranar 4 ga watan Oktoban 2017, inda suka halaka sojin Amurka 4 da na Nijar 5.

Tun bayan farmakin waccan lokacin har yanzu babu wanda aka kama, dake da alaka da harin na Tongo Tongo.

Cikin watan Nuwamban 2017 wasu majiyoyi daga Amurka suka ce bayanan da kwamandodin sojin kasar suka gabatar kan yadda dakarunsu 4 suka mutu a Nijar ya sabawa asalin abinda ya faru.

Bayanan na baya baya sun nuna cewar, dakarun sun je inda aka samu hadarin ne domin kama wani kwamandan ‘yan ta’adda da ake kira Dandou cikin dare.

Janar Dunford yace sojojin Amurka 12, na tawagar tare da sojojin Nijar 30, lokacin da ‘yan tawayen 50 dake da alaka da kungiyar IS suka kai musu hari a Tongo Tongo.

Hafsan yace sojojin sun dauka zasu iya murkushe maharan ne ya sa basu nemi akai musu dauki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.