Isa ga babban shafi
Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta janye tuhume-tuhume daga kan 'yan adawa

Jagoran jam'iyyar adawa ta MRC a Kamaru Maurice Kamto.
Jagoran jam'iyyar adawa ta MRC a Kamaru Maurice Kamto. AFP Photo/MARCO LONGARI

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya bada umarnin janye tuhume-tuhumen da ake yiwa wasu jagororin ‘yan adawa kasar, ciki har da na jam’iyyar MRC dake karkashin jagorancin babban abokin hamayyarsa Maurice Kamto da a yanzu ke tsare.

Talla

Yayinda yake sanar da matakin Paul Biya ya ce afuwar ta shafi wadanda suka shirya zanga-zangar turjiya ga sakamakon zaben shugabancin kasar ne a shekarar bara, sai dai jawabin shugaban na Kamaru, bai fayyace ko afuwar za ta shafi jagoran ‘yan adawar Maurice Kamto ba, wanda yayi ikirarin lashe zaben.

A ranar Alhamis shugaba Paul Biya ya bada umurnin dakatar da shari’ar da ake yiwa daruruwan 'yan aware dake neman ballewa domin kafa kasa ta kansu ta masu amfani da turancin ingilishi.

Fira minista Joseph Dion Ngute ya shaidawa taron kasar kan sansanta rikicin 'yan aware masu amfani da turancin ingilishi cewar shugaban ya bada umurnin sakin mutane 333 da lamarin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.