Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sace mutane shida a Adamawa

Rundunar 'yan sandan Adamawa a Najeriya ta tabbatar da lamarin
Rundunar 'yan sandan Adamawa a Najeriya ta tabbatar da lamarin Reuters

A Najeriya, wasu ‘yan bindiga sun sace mutane 6 a jihar Adamawa, a wani kauye da ke kusa da kan iyakan kasar da Jamhuriyar Kamaru.

Talla

Wasu mazauna kauyen Gurin, da ke karamar hukumar Fufore a jihar ta Adamawa sun ce ‘yan bindigan da suka shigo da dama sun yi awon gaba da matasa shida.

Sai dai da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Nguroje ya ce maharan sun shiga kauyen kuma sun tafi mutane 3; yana mai cewa da farko mutane 4 suka sace, amma suka saki daya don ya kai labari.

Satar mutane don karbar kudin fansa ta ta’azzara a cikin ‘yan makonnin nan a jihar Adamawa, inda ba da dadewa ba aka kashe wani jagoran Fulani, Abdul Bali, tare da sace wani malami da ke koyarwa jami’ar Modibo Adama har sai daya biya naira miliyan 2 kafin aka sake shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.