Isa ga babban shafi
Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da sace mutane 200 a Congo

Makaman 'yan bindigar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
Makaman 'yan bindigar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane kusan 200 aka sace a yankin Arewa Maso Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekara.

Talla

Ofishin jinkai na majalisar da ake kira OCHA ya bayyana cewar kungiyoyin Yan bindigar da ke dauke da makamai sun sace mutane 183 a Yankin Haut-Uele da Bas-Uele cikinsu har da yara kanana 34, yayin da wasu yan bindigar dabam kuma suka sace fararen hula 11, cikin su harda yara 5.

Yankin Arewaci da kudancin Kivu da ke dauke da tarin kungiyoyin Yan bindiga na fama da matsalar satar mutane ana garkuwa da su.

A shekarar 2018 sau 76 aka sace mutane a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.