Isa ga babban shafi
Duniya

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya lashe kyautar Nobel

Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed AFP/Monirul BHUIYAN

A yau juma'a,kwamitin da ke da nauyin tantance mutanen da suka dace su lashe kyautar Nobel sun bayyana Firaministan Habasha Abiy Ahmed a matsayin wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya. 

Talla

Firaministan Habasha na daya daga cikin mutanen da suka taka gaggarumar rawa wajen sulhunta kasar sa Habasha da Erythrea.

Kasashen sun koma aminan juna ne ranar 9 ga watan yuli bayan share kusan shekaru 20 suna kai ruwa rana.

A kasar Saudiya ne Firaministan Habasha da Shugaban kasar Erythrea suka rattaba hannu a takardar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Abiy Ahmed mai shekaru 43 dan kabilar Oromo ya samu mukamin Firaministan kasar ne a watan afrilun shekarar 2018.

Da samun wannan labari,Firaministan kasar Habasha ya nuna farin cikin sa tareda bayyana kyautar a matsayin kyauta zuwa nayihar Afrika

A cikin shekarar nan Gwamnatin kasar Habasha ta sanar da kashe mutumin da ake zargi da kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, a Yankin Amhara, bayan kashe babban hafsan sojin kasar da kuma shugaban Yankin.

Ofishin Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana mutumin a matsayin Asaminew Tsige wanda aka taba daurewa da irin wannan yunkuri kafin Firaminista Ahmed ya sake shi a karkashin shirin sa na yiwa jama’a afuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.