Isa ga babban shafi
Afrika

Zaben Shugaban kasar Tunisia

Zaben shugaban kasar Tunisia a yau Lahadi
Zaben shugaban kasar Tunisia a yau Lahadi RFI/Michel Picard

A yau mutanen Tunisia ke kada kuri’a don zaben sabon Shugaban kasar .Zaben da ya hada yan takara biyu da suka hada da Nabil Karoui attajiri dake fuskantar tuhuma dangane da kaucewa biyan haraji wanda zai fafata da Kais Saled malamin kuma masanin dokkokin shara’a.

Talla

Hukumar zaben kasar ta samun yiwa mutane milyan 7 rijista da kuma suka karbi katunan zabe.

Mako daya kenan da aka gudanar da zaben yan majalisu, hasashen masana siyasar kasar ta Tunisia na nuni cewa zaben zai iya bayar da mamaki, kasancewar kowane bangare kan iya bayyana nasarar sa yan lokuta da kamala shi.

An dai bude ruhunan zabe da safiyar yau lahadi ba tareda an fuskanci wata matsalla ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.