Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Guillaume Soro, zai tsaya takarar shugabamcin kasar Cote d'Ivoir a 2020

Guillaume Soro, tsohon shugaban majalisar dokokin kasar cote d'Ivoire.
Guillaume Soro, tsohon shugaban majalisar dokokin kasar cote d'Ivoire. © RFI

Guillaume Soro, tsohon shugaban ‘yan tawayen kasar cote d’ivoire, haka kuma tsohon shugaban majalisar dokokin kasar, da ya rikide yaama dan adawa, ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugabancin kasar a 2020.

Talla

Tuni dai ake ganin zai iya samun goyon bayan kungiyar Générations et peuples solidaires (GPS). Guillaume Soro ya bayyana aniyar tasa ta son tsayawa takarar ne, a cikin wata firar hadin guiwa da ta hadashi da kafafen yada labaran Faransa, a jiya, cewa da Radio France Inernatioale   RFI da tashar talabijinta France 24

Kimanin shekaru 2 da suka gabata ne dai, aka samu Baraka tsakanin Guillaume Soro da shugaba Alhasan Watara, da ake ganin yana kokarin sake yin wani wa’adi na 3,a jere, duk da cewa  bai furta ba haka ba, amma  kuma bai kawar da yiyuwar fsake tsayawarba bayan da kundin tsarin mulkin kasar ya bashi damar yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.