Isa ga babban shafi
Kamaru

Sojojin Kamaru sun musanta yiwa mata masu goyo kisan gilla

Hoton bidiyon dake nuna yadda wasu sojoji suka yiwa wasu mata 2 da 'ya'yansu kisan gilla a watan Yuli na shekarar 2018.
Hoton bidiyon dake nuna yadda wasu sojoji suka yiwa wasu mata 2 da 'ya'yansu kisan gilla a watan Yuli na shekarar 2018. Daily Mail

Kotun sojan Kamaru dake birnin Yaounde ta dage zaman shari’ar sojojin kasar 7 da ake tuhuma da yiwa mata biyu da ‘ya’yansu kisan gilla, zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba, 2019.

Talla

A watan Yuli na 2018, wani bidiyo ya nuna yadda sojoji cikin kakinsu, suka halaka wasu mata 2, daya dauke da goyo, daya kuma mai yaro karami, ta hanyar bude musu wuta, a yankin Zeleved dake arewa mai nisa a kasar ta Kamaru.

Bidiyon a waccan lokacin ya tayar da kura kan zarge-zargen tauye hakkin dan adam kan fararen hula da ake yiwa jami’an tsaron dake yakar ta’addanci.

Da fari gwamnatin Kamaru ta bata amince da sahihancin bidiyon ba, sai dai daga bisani cikin watan Agusta, ta bada umarnin soma bincike kan bidiyon wadda a karshe ta tabbatar da sahihancinsa, tare da kame jami’an sojin 7 da suke da alaka da kisan gillar.

Sai dai bayan gurafanar da su gaban kotun soja, sojojin 7 sun ki amincewa da tuhumar da ake musu na aikata kisan gilla.

Kotun ta tsayar da 4 ga watan Nuwamban a matsayin lokacin daza ta ci gaba da zaman sauraron shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.