Isa ga babban shafi
Sudan

Al'ummar Sudan na neman gwanati ta soke Jam'iyyar al-Bashir

Al'ummar Sudan a dandalinsu na zanga-zanga kan neman gwamnati ta haramta Jam'iyyar tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir.
Al'ummar Sudan a dandalinsu na zanga-zanga kan neman gwamnati ta haramta Jam'iyyar tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir. ASHRAF SHAZLY / AFP

Dubban 'yan kasar Sudan sun gudanar da zanga zanga a biranen kasar, cikin su harad birnin Khartoum inda suke bukatar sabuwar gwamnati ta rusa Jam’iyyar tsohon shugaban kasa Omar Hassan al Bashir.

Talla

Masu zanga zangar da suka hada da mata da maza a biranen Khartoum da Omdurman da Madani da Al Obeid da Port Sudan sun bayyana goyan bayan su ga sabuwar gwamnatin da aka dorawa alhakin shirya mayar da mulki ga hannun farar hula.

Gangamin mau ya kuma bukaci yin adalci ga mutane da aka kashe Yan uwan su lokacin zanga zangar da ta kifar da gwamnatin shugaba Al Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.