Isa ga babban shafi
Senegal

Khalifa Sall zai koma fagen siyasa bayan zaman wakafi

Khalifa Sall yayin wani taron manema labarai bayan fitowa daga gidan kaso.
Khalifa Sall yayin wani taron manema labarai bayan fitowa daga gidan kaso. SEYLLOU / AFP

Tsohon Magajin Garin Dakar da ke Senegal, Khalifa Sall da shugaban kasa Macky Sall ya yiwa ahuwa bayan daurin shekaru biyu da rabi a gidan yari, ya bayyana cewar zai cigaba da harkokin siyasar sa kamar yadda ya saba.

Talla

Yayin da ya ke jawabi ga dimbin magoya bayan sa da kuma 'yan Jaridu, Sall ya ce duk da daurin da aka masa, wanda ya haramta masa ‘yancin shiga harkokin siyasa, ba zai sashi dainawa ba.

Dokar Senegal ta haramtawa wanda kotu ta samu da laifi shiga harkokin siyasa, ganin cewa kotu ta daure tsohon Magajin Garin shekaru 5 a gidan yari saboda samun sa da laifin almubazzaranci da kudin da ya kai euro miliyan biyu da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.