Isa ga babban shafi
Kamaru-Bamenda

An tsinci kan dan sanda babu gangar jiki

Wasu 'yan sandan Kamaru a yankin masu amfani da turancin Ingilishi.
Wasu 'yan sandan Kamaru a yankin masu amfani da turancin Ingilishi. AFP/STR

An tsinci kan wani jami’an ‘yan sandan kasar Kamaru ba tare da gangar jikinsa ba a birnin Bamenda, hedikwatar yankin Arewa maso Yamma, daya daga cikin jihohin kasar da ake amfani da Turancin Ingilishi mai fama da rikicin ‘yan aware.

Talla

Majiyar tsaron Kamaru dai ta daura alhakin kissan jami’an dan sandan Paul Nwana, a daren jiya Lahadi, kan mayakan ‘yan aware dake neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia.

Rahotanni sun ce kan jami’in tsaron yana dauke raunuka da dama, abinda ke nuna alamun cewar an azabtar da dan sandan kafin yi masa kisan gillar.

Wannan na zuwa ne kasa da makwanni uku, bayan kisan gillar da aka yi wa Frorence Ayafor jami’ar tsaron gidan kaso, ita ma a birnin na Bamenda, matakin da ya kai kashen duniya sukayi Allah wadai da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.