Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Yunwa ta hallaka giwaye 55 a gandun dajin Zimbabwe

Wasu giwaye a gandun dajin Zimbabwe
Wasu giwaye a gandun dajin Zimbabwe Pixabay/CC0/designerpoint

Akalla Giwaye 55 suka mutu a Zimbabwe sakamakon tsananin farin da ya afkawa kasar, wanda ya haifar da rashin abinci da ruwan sha.

Talla

Kakakin hukumar kula da gandun dajin kasar, Tinashe Farawo ya ce daga watan Satuma zuwa yanzu, giwaye 55 suka mutu a Gandun Dajin Hwange.

Jami’in ya ce anyi gandun dajin ne domin aje giwaye 15,000, amma yanzu haka suna da giwayen da suka zarce 50,000.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kashi daya bisa uku na al’ummar Zimbabwe, wato mutane sama da miliyan 5 ke fuskantar barazanar karancin abinci kafin lokacin girbin da za’ayi a shekarar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.