Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Al’ummar Zimbabwe na zanga-zanga kan takunkuman EU da Amurka

Wasu masu zanga-zanga a Zimbabwe.
Wasu masu zanga-zanga a Zimbabwe. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Dubun dubatar al’ummar kasar Zimbabwe na shirin tsunduma zanga-zangar adawa da halin matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki sakamakon yawaitar takunkuman karya tattalin arzikin da Tarayyar Turai da Amurka suka kakaba mata.

Talla

Mahukuntan Zimbabwe wadanda ke dora alhakin halin da kasar ke ciki kan takunkuman da ke kanta, tuni suka ayyana yau Juma’a a matsayin ranar hutu don gudanar da zanga-zangar.

Wasu bayanai sun bayyana cewa manyan motoci da dama ne suka bazu a yankunan kasar 10 don dakon mutane zuwa Harare babban birnin kasar wajen da zanga-zangar za ta gudana.

A shekarar 2002 ne Amurka ta kakabawa Zimbabwe takunkumi sakamakon zargin take hakkin bil’adama baya ga kwace gonakin fararen fata, takunkuman da suka shafi jami’an gwamnatin kasar da dama ciki har da shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa.

Gwamnatin Zimbabwe dai ta bayyana cewa takunkuman sun haddasawa kasar asarar biliyoyin daloli baya ga hana mata kudaden shiga da kuma matakin da ya haddasa mata fuskantar koma baya ta fuskar albarkatun da ake shigar mata ciki har da man fetur lantarki da kuma ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.