Isa ga babban shafi

Kamaru na shirin maidawa Bolere tafiyar da tashar jiragen ruwar kasar da ta kwace a baya

Tashar jiragen ruwan birnin Douala na kasar Kamaru
Tashar jiragen ruwan birnin Douala na kasar Kamaru Reinnier KAZE/AFP

Gwamnatin Kamaru ta bukaci dakatar da shirin mika kwangilar tafiyar da ayukkan tasha ruwan Douala wa kamfanin TIL mallakar kasa Swisland har sai an jira hukuncin kotu,biyo bayan wata kara da hadakar kamfanonin Bollore na attajirin kasar Faransa Vincent Bollore ya shigar ya na mai kalubalantar hukuncin wata kotu a birnin Douala.

Talla

A cikin wata takardar sako da kanfanin dillancin labarai Fransa AFP ya tabbatar da sahihanci ta,  a wata majiyar tashar ruwan Douala, Fadar gwamnatin Kamaru ta bukaci a jingine karasa kwangilar da ake shirin dankawa kamfanin TIL har sai an jira hukunci kotu, bayan wata kara da kanfanin Bollore wanda ya shafe shekaru 15 yana tafiyar da aikin tashar ruwan ta hanyar gungun kamfanonin Bollore-APM-TERMINAL ya shigar a gaban kotu.

Wanan matakin hukumomin Kamaru dai,na zuwa ne bayan wata ziyarar yini biyu da Ministan harakokin wajan Faransa Jean Ive le Drian ya kammala a kasar, inda ya isar da korafe korafen kanfanonin kasa Faransa dake fuskanta dinbin matsaloli a kasar ta shugaba Paul Biya.

A watan Janairu ne aka ware kanfanin na Bollore daga cikin jerin kafanonin da suka bayyana shawar su na samun kwangilar tafiyar da tashan ruwan Douala, abunda ya tilasta masa daukaka kara a gaban kotu tareda yin nasarar dakatar da shirin ranar 16 ga watan Agusta.

Tashar ruwan Douala a kasar ta Kamaru, ita ce mafi girma a fadin din tsakiyar Afirka, inda ake jigilar kayayyaki daga kasashen Tchadi da kuma Afirka ta tsakiya, kasashe biyu makwafatan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.