Isa ga babban shafi
Najeriya

wakilin RFI Hausa a Abuja Aminu Manu ya rasu

Aminu Manu, wakilin RFI a Abuja, Najeriya da Allah ya wa rasuwa
Aminu Manu, wakilin RFI a Abuja, Najeriya da Allah ya wa rasuwa RFI/Hausa

RFI Hausa ta yi rashin daya daga cikin wakilan ta da ke aiko rahotanni daga Abuja, Aminu Ahmad Manu, wanda Allah Ya yiwa rasuwa yau a birnin Abuja dake Najeriya.

Talla

A shekaru 12 da ya yi yana aiki da RFI Hausa, Aminu Manu ya zama wakili a Plateau da Nasarawa, kafin daga bisani ya koma Abuja, inda ya ke aiko da rahotanni daga Majalisar dokokin Najeriya da Hukumar Zabe da kuma Shelkwatar Rundunar Sojin kasar.

Marigayin na daya daga cikin zaratan wakilan da RFI Hausa ke alfahari da su saboda irin gudumawar da suka bayar wajen habakar tashar a fadin duniya.

Da fatan Allah Ya gafarta masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.