Isa ga babban shafi
Ta'addanci

Farmakin 'yan ta'adda kan sojoji ya tsananta a yankin Sahel

A baya-bayan 'yan ta'addan sun kashe sojojin Mali kimanin 50
A baya-bayan 'yan ta'addan sun kashe sojojin Mali kimanin 50 AFP

'Yan ta'adda sun sake kaddamar da wani sabon farmaki a Burkina Faso,inda suka kashe jami'an tsaro biyar,  harin da ke zuwa a daidai lokacin da ake zaman makoki a Mali biyo bayan kisan da 'yan ta'ddan suka yi wa sojojin kasar kimanin 50. 

Talla

Kazakila mayakan masu ikirarin jihadi sun kai makamancin wannan harin Jancinsa a jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka sojojin kasar 12, lamarin da ya sa ake diga ayar tambaya dangane da amfani ko rashin amfanin dubban dakarun kasashen Yammacin Duniya da ke jibge a cikin wadannan kasashe na yankin Sahel.

Ko a Najeriya, mayakan sun sha kaddamar da irin wannan farmakin kan jami'an tsaro musamman a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

A yayin zantawa da sashen hausa na RFI, Alkassoum Abdourahman mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Jamhuriyar Nijar, ya ce, muddin ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, wasu yankuna za su bukaci ballewa daga wadannan kasashe domin cin gashin kansu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi da Alkassoum Abdourrahman.

Alkassoum Abdourahman mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, kan yawaitan hare-hare a yankin Sahel

Masharhancin ya ce, 'yan ta'addan na samun karin goyon baya daga kungiyoyin'yan ta'adda na wasu kasashen duniya kamar Syria wadda ta kasance cibiyar mayakan IS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.