Isa ga babban shafi
Wasanni

Sadio Mane gwarzon Afrika na shekara ta 2019

Sadio Mane Dan wasan kwallon kafa
Sadio Mane Dan wasan kwallon kafa RFI/Hausa

Jiya talata ne aka gudanar da bikin karrama gwarzon dan kwallon Afrika a kasar Masar, dan wasan Liverpool, wato Sadio Mane ne ya lashe wannan kyauta a gaban Mohammed Salah na Masar da Rihad Mahrez daga Algeria.

Talla

Sadio Mane dan wasan Senegal mai shekaru 27 wanda bai samu nasarar lashe kyautar nan ta ballon d’or a gaban Lionnel Messi duk da irin jajircewa da kuma rawar da ya taka a Duniyar kwallon kafa, inda a jimilce ya zura kwallaye 34 a raga a shekara ta 20149 ,ya kuma taimaka wa kungiyar sa Liverpool wajen lashe wasanni.

Yan wasa uku ne suka shiga layin neman wannan kyauta a bikin da ya gudana a Masar, Sadio Mane daga Sanegal, Mohamed Salah daga Masar sai Riyad Mahrez daga Aljeriya.

Dukkanin ‘yan wasan uku sun nuna bajinta a shekarar 2019, inda Salah da Mane suka lashe kofuna da suka hada da kofin gasar zakarun Turai da UEFA Super Cup da kuma kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyin duniya .

Shi kuma Mahrez ya taimaka wa kungiyarsa ta Manchester City sake lashe gasar firimiyar ingila, yayin da ya taimaka wa kasar sa ta Algeria lashe gasar cin kofin Afrika a karon farko cikin shekaru 29, tareda doke Senegal .

Gwarzon dan wasa Sadio Mane,kungiyar da ta haska a shekarar itace kungiyar kwallon kafar Algeria.

Djamel Belmadi mai horar da kungiyar kwallon kafar Algeria ne ya lashe kyautar gwarzon mai horar da kungiyar kwallon kafa na shekarar da ta shude Dan wasa mafi kakkantar shekaru shine Achraf Hakimi daga Morocco.

Dan wasan da ya haska daga cikin masu taka tamola a wata kungiya dake Nahiyar shine Youcef Belaili daga Algeria.

Shugaban kungiyar kwallon kafa da ya haska a nahiyar Afrika shine Moise Katumbi na kungiyar TP Mazembe daga Congo.

Yar Najeriya Asisat Oshoala daga Najeriya ce yar wasa bangaren mata da ta lashe kyautar daga hukumar Caf.

Sadio Mane ne dan Senegal na biyu wanda ya shiga jerryn yan wasan kasar baya ga Elh Diuof da ya taba lashe irin wannan kyauta daga hukumar Caf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.