Isa ga babban shafi
Afrika

Boko Haram ta kashe mutane 6 a Dikwa

Sanssanin yan gudun hijira a Dikwa
Sanssanin yan gudun hijira a Dikwa STRINGER / AFP

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane biyar tareda yin awon gaba da wasu can daban a wani kazamin hari da suka kai garin Dikwa dake da nisan kilometa 90 da Maiduguri a jihar Borno.

Talla

Mutanen da harin ya ritsa da su na daga cikin mutanen da suka shiga dajin wajen neman itacen girki, yan boko Haram sun ritsa da su inda nan take suka kashe mutane biyar a cewar Babakura Kolo memba ne a kungiyar yan sa kai.

Garin Dikwa ya kasance wanin sanssani da aka girke yan gudun hijira dubu 70 da matsallar tsaro ya tilastawa baro matsugunin su da kuma ke rayuwa a karkashin kungiyoyin agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.