Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashin shaidu ya tilasta dage shari'ar masu auren jinsi a Lagos

Alamar kotun Najeriya.
Alamar kotun Najeriya. The Guardian

Rahotanni daga Lagos a Najeriya sun ce rashin bayyanar shaidu a gaban kotu ya hana cigaba da sauraron tuhumar da ake yiwa wasu mutane 47 kan luwadi ko kuma auren jinsi a Jihar, laifin da ke dauke da hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Talla

Tun cikin watan Agustan 2018 ne aka kame mutanen a wani otel da ke Lagos amma kuma kawo yanzu sun ki amincewa da tuhumar da ake musu ta aikata luwadi da ke matsayin babban laifi a Najeriya.

Haka zalika duk da yadda aka kama su da hannu wajen shigar da wasu matasa harkar ta luwadi ko kuma auren jinsi mutanen sun ki amsa laifin yayinda ake ci gaba da jan shari'a

Shari'ar ta yau karkashin mai shari'a Rilwan Aikawa kotun ta sanar da dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Maris mai kamawa don ci gaba da sauraron shari'ar tare da halartar shaidu.

Najeriya dai na sahun kasashen da suka haramta luwadi ko kuma auren jinsi ta kowacce fuska yayinda hukuncin daurin akalla shekaru 14 a gidan yari ke hawa kan duk wanda aka samu da aikata laifin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.