Isa ga babban shafi
Najeriya-Abacha

Tababa ta baibaye yadda Najeriya za ta kashe kudin Abacha da ta karbo

Majalisar dattijan Najeriya.
Majalisar dattijan Najeriya. Nigeria National Assembly

Gwamnatin Najeriya ta ce kudin da Amurka ta mayarwa Najeriya da suka kai Dala miliyan 318 daga kudin Abacha za’ayi amfani da su wajen fadada gina hanyar motar Lagos zuwa Ibadan da hanyar Abuja zuwa Kano da kuma cigaba da ginin gadar Onitsha.

Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana haka a sanarwar da mai taimaka masa a bangaren yada labarai Umar Gwamndu ya sanyawa hannu.

Tuni wannan matsayi ya haifar da mahawara, inda wasu ke cewa lokaci yayi da za’a zuba wadannan makudan kudade zuwa wasu hanyoyi na daban, maimakon wadannan da aka kwashe dogon lokaci ana kashe musu.

Dangane da wannan mahawara, mun tattauna da Barrister Lawal Ishaq, lauya mai zaman kan sa, kuma ga tsokacin da yayi akai.

Tababa ta baibaye yadda Najeriya za ta kashe kudin Abacha da ta karbo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.