Isa ga babban shafi
AU-Ta'addanci

Hussaini Monguno kan gazawar AU wajen magance matsalar tsaro

Wakilan kasashen Tarayyar Afrika yayin taron AU da ke gudana a Addis Abba na Habasha.
Wakilan kasashen Tarayyar Afrika yayin taron AU da ke gudana a Addis Abba na Habasha. RFI/Miguel Martins

Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta amsa gazawa wajen yakar ayyukan ta’addancin da ke kara tsananta a kasashen nahiyar, bayanda a yanzu haka aka cika shekaru 7 da alkawarin da ta dauka na gaggauta kawar da kalubalen tsaron da kasashen na AU ke fuskanta.

Talla

Yayin taron shekara-shekara na kungiyar karo na 33 da ke gudana can a birnin Addis Ababa na Habasha, shugaban hukumar gudanarwar AU Moussa Faki Mahammat ya bayyana cewa a yanzu haka kasashen Tarayyar Afrika na bukatar tallafin ketare don tunkarar matsalar tsaro.

Taron na AU wanda ya faro da sharar fagen ganawar ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar 55 tun daga jiya Alhamis ya tattauna yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara duk kuwa da alkawarin kungiyar na ganin ta magance matsalar kafin shekarar nan da muka shiga ta 2020.

Danganne da wannan batu ne Ahmed Abba ya tattauna da Hussaini Monguno masanin harkokin tsaro a Najeriya ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.

Hussaini Monguno kan gazawar AU wajen magance matsalar tsaro

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.