Isa ga babban shafi
Afrika

A watan afrilu,kotu za ta yanke hukunci dangane da kisan wasu mutane a Guinee

Wasu daga cikin ma'aikatan hakar  ma'adinai a Afrika
Wasu daga cikin ma'aikatan hakar ma'adinai a Afrika Olivier Polet/Corbis via Getty Images

Wata kotun kungiyar kasashen Afrika ta yamma ta ce a watan Afrilu mai zuwa za ta yanke hukunci kan zargin yi wa wasu mutane 6 kisan gillar da ake wa hukumomin kasar Guinea da wani kamfanin kasar Brazil a shekarar 2012.

Talla

Mutane shidan sun mutu ne bayan ‘yan sanda sun bude musu wuta yankin Zogota na kasar Guinea yayin zanga – zangar adawa da suke da yadda kamfanin hakar ma’adinai na Brazil ke daukar ma’aikata.

A zaman da kotun ta yi a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja a Alhamis dinnan ne ta sanar da ranar yanke hukunci.Kungiyoyin kare hakokin bil Adam na fatan kotu za ta yi adalci wajen yanke hukunci dangane da wannan kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.