Isa ga babban shafi
Afrika

Al'ummar Kamaru na kada kuri'a a zaben 'yan Majalisu

Wasu daga cikin masu lura da zabe a kasar Kamaru yayin muhara dangane da zaben yan Majalisu
Wasu daga cikin masu lura da zabe a kasar Kamaru yayin muhara dangane da zaben yan Majalisu Stringer / AFP

Kusan mutane milyan bakwai ne suka karbi katunan su na zabe a Kamaru,dangane da zaben yan Majalisau da na wakilan kananan hukumomi dake gudana ayau Asabar,zaben da wasu jam’iyyun siyasa suka bukaci kauracewa don nuna adawar su da sakamakon zaben shugabanci da ya gabata.

Talla

Matakin kauracewa zaben daga jam’iyyar Maurice Kamto ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ya’an jam’iyyar, yayinda wasu rahotanni daga yankunan yan aware na nuni cewa mutane da dama ne suka gudun daga gidajen su sabili da matsallar tsaro.Da dama daga cikin yan sa ido basu samu takardar izinin aikewa da wakilai zuwa ruhunan zabe a fadin kasar.

A wasu yankunan kasar ta Kamaru ana bayyana cewa jam’iyyar Shugaban kasar ce keda yan takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.