Isa ga babban shafi
Benin

'Yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sandan Benin

Wasu jami'an 'yan sandan Jamhuriyar Benin.
Wasu jami'an 'yan sandan Jamhuriyar Benin. YANICK FOLLY/AFP/Getty Images

Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari tashar ‘Yan Sandan Jamhuriyar Benin dake kusa da iyakar Burkina Faso, inda suka jikkata jami’i guda.

Talla

Yan Sandan Keremou dake kusa da garin Banikoara sun ce ‘yan bindiga 10 ne haye kan babura suka kai harin ta hanyar bude wuta da bindigogi masu sarrafa kansu.

Rundunar ‘yan sandan Benin ta ce jami’anta hudu a ofishin na Keremou a lokacin da ‘yan bindigar suka afka musu, lamarin da yayi sanadin jikkatar guda.

A shekarar 2019 ‘yan bindiga suka sace wasu Faransawa 2 dake yawon bude ido a kasar ta Benin akan iyaka da Burkina Faso.

Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel dake fama da matsalar hare-haren ‘yan bindigar da a baya bayan nan suke karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.