Isa ga babban shafi
Afrika

Gwamnatin Mali za ta shiga tattaunawa da yan Tawayen arewaci

Ibrahim Boubacar Keita, Shugaban kasar Mali
Ibrahim Boubacar Keita, Shugaban kasar Mali RFI-France 24

Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana tintibar yan tawayen kasar da zummar tattaunawar da zata haifar da zaman lafiya bayan daukar dogon lokaci ana kashe mutane a sassan kasar.

Talla

Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Keita ya bayyana cewa ya nada tsohon shugaban kasar Dioncounda Traore domin tattaunawa da Yan bindigar domin kawo karshen asarar rayukar da ake tafkawa a kasar.

Kungiyoyi da dama sun dade suna kira ga gwamnatin Mali da shiga tattauna da Yan tawayen domin ganin sun aje makaman su da kuma rungumar zaman lafiya, cikin su harda kungiyar ICG.

A daya wajen a jiya ne rundunar sojin Mali ta fara tura dakarun ta a Kidal dake yankin arewacin kasar ta Mali domin karbar tafiyar da ikon wannan birni mai matukar muhimmanci da ya fice daga hannun mahukumtan kasar na tsawon lokaci .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.