Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Boko Haram sun kashe mutane a kauyen Auno

Daya daga cikjin kauyukan Maiduguri
Daya daga cikjin kauyukan Maiduguri Fati Abubakar/RFI

A Najeriya, kimanin mutane 30 ne mayakan Boko Haram suka hallaka tare da yin awon gaba da wasu mata da kananan yara da dama a wani hari da suka kai a daren jiya lahadi a kauyen Auno da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Talla

Da misalign karfe 10 na daren jiya litinin ne dai mayakan na Boko Haram suka afkawa ayarin matafiya wadanda sakamakon rufe hanyar da ta hada Maiduguri zuwa Damaturu ya sa su kwana a garin na Auno mai nisan kilomita 20 daga Maiduguri fadar gwamanatin jihar Borno.

Bilyamin Yusuf wakilin mu daga yankin ya aiko mana da wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.