Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya ziyarci Maiduguri don yiwa jama'a jajen harin Auno

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan isarsa Maiduguri don jajantawa al'umma game da harin Auno da Boko Haram ta kashe mutane fiye da 30 baya ga kone motoci da tarin dukiya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan isarsa Maiduguri don jajantawa al'umma game da harin Auno da Boko Haram ta kashe mutane fiye da 30 baya ga kone motoci da tarin dukiya. RFI/Hausa

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari yau ya ziyarci Maiduguri dake Jihar Barno domin jajantawa al’ummar Jihar kan kazamin harin da mayakan kungiyar boko haram suka kai Auno wanda ya kashe mutane sama da 30.

Talla

Buhari na wannan ziyarar ce kwanaki 3 bayan afkuwar lamarin saboda halartar taron kungiyar kasashen Afirka da ya tafi a Addis Ababa.

Gwamnan Jihar Barno, Farfesa Babagana Zulum da manyan hafsoshin tsaro da jami’an gwamnati suka tarbi shugaban a tashar jiragen sama, kafin daga nan ya zarce fadar Shehun Barno domin mika sakon ta’aziyyar sa da na gwamnatin Najeriya kan kazamin harin da aka samu a Auno.

Wannan harin ya haifar da mummunar suka kan matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka kan yaki da kungiyar boko haram, inda wasu mutane da dama ke bukatar ganin gwamnati da rundunar sojin kasar sun sake fasali kan yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.