Isa ga babban shafi
Mali-Ta'addanci

Harin 'yan bindiga ya hallaka fararen hula 20 a Mali

Dakarun Sojin Mali a yankin gabashin kasar mai fama da rikici.
Dakarun Sojin Mali a yankin gabashin kasar mai fama da rikici. AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES

Rahotanni daga Mali sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 20, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai garin Ogo-sagou da ke tsakiyar kasar cikin daren jiya alhamis.

Talla

Bayanan farko a game da wannan hari na nuni da cewa lamari ne mai alaka da kabilanci, domin kuwa garin Ogo-sagou mazaunansa Fulani ne, inda a cikin watan maris na shekarar bara ‘yan kabilar Godon suka kai hari tare da kashe fararen hula akalla 160 a kauyen.

Hakimin garin Aly Ousman Barry, ya ce akalla mutane 30 ne dauke da makamai suka afka wa garin inda suka yi barin wuta akan mutane tare da cinna wa gidaje wuta kafin su arce.

Da farko an bayyana cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu a harin, to sai dai wani jami’in gwamnatin a yankin ya ce an kirga gawarwakin mutane 20, yayin da wasu akalla 28 suka bata baya ga wadanda aka raunuta.

Ga alama maharan sun yanke shawarar afkawa mazauna garin na Oga-sagou ne sa’o’i kadan bayan da suka samu labarin cewa jami’an tsaron da ke bai wa jama’a kariya sun fice daga garin. Mali dai kas ace da ke fama da ayyukan ta’addanci da kuma rikici tsakanin kabilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.