Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Mutane miliyan 3 na bukatar agajin gaggawa a Nijar - MDD

Wasu 'yan gudun hijira da rikici ya tilasta wa zuwa Nijar daga Najeriya.
Wasu 'yan gudun hijira da rikici ya tilasta wa zuwa Nijar daga Najeriya. REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane miliyan uku ne a Nijar, wadanda fiye da rabin su kananan yara ne ke bukatar agajin gaggawa saboda hukubar da suke sha sakamakon bala’o’i da rikice rikice da ke faruwa a yankunansu.Michael Kuduson na dauke da karin bayani.

Talla

A wata sanarwa, asusun kula da kananan yara na UNICEF ya zayyano irin hatsarin da al’ummar ke ciki sakamakon matsalar tsaro, rashin abinci mai gina jiki, yawaitar bullar cutuka da annoba, ambaliyar ruwa, fari da asarar matsugunai a matsayin ummul’aba’isan barazanar da mutane miliyan biyu da dubu dari 9, ciki har da yara miliyan daya da dubu dari 6 ke fuskanta.

Jami’a mai bada shawara kan samar da abinci mai gina jiki na UNICEF a yankin Sahel, Felicite Tchibindat ta ce wutar rikici na ci kamar wutar daji a yankin na Sahel, biyo bayan ziyarar da ta kai jihar Diffa, inda ta koka da yadda mata da yara ne ke shan bakar wahala.

Tun a shekarar 2015 Nijar ke fuskantar matsalar hare hare na ‘yan ta’adda a kusa da iyakarta da Mali da Burkina Faso, lamarin da ke ta’azzara bukatar taimakon jinkai a yankunan Tillaberi da Tahoua, inda rikici ya daidaita kusan mutane dubu 78.

Nijar ta baiwa ‘yan gudun hijira kusan dubu dari 4 da 50 matsuguni, wadanda cikinsu akwai ‘yan Najeriya, Mali, da Burkina Faso, da kuma wasu daga cikin kasar, wadanda ‘yan ta’adda suka daidaita.

A kudu maso gabashin kasar mata 15 da yara 5 ne aka take har lahira yayin wani turmutsitsi wajen rabon abinci da kudi ga ‘yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.