Isa ga babban shafi
Afrika-WHO

WHO ta koka da matakan Afrika na tunkarar Coronavirus

Likitocin da ke kula da masu fama da cutar corona a China.
Likitocin da ke kula da masu fama da cutar corona a China. Noel Celis/Pool via REUTERS

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana damuwa kan shirin da kasashen Afirka ke da shi wajen fuskantar coronavirus ko kuma COVID-19 idan an samu barkewar ta a kasar.

Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya bukaci kasashen Afirka da su hada kan su wajen daukar kwararan matakan tinkarar cutar.

Yayin ganawa da ministocin lafiyar Afirka a Addis Ababa, Gebreyesus ya ce su na cikin fargaba dangane da samun cutar a Afirka lura da irin matsalolin da suka dabaibaye harkokin kula da lafiyar jama’a a nahiyar.

Ya zuwa yanzu cutar ta hallaka mutane sama da 2,200 a China bayan ta kama mutane sama da 75,500, yayin da aka samu mutane 1,150 da suka kamu da cutar a wajen China.

Kasar Masar ce kasa daya tilo da ta sanar da samun cutar a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.